A cikin shekaru biyu na farko a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, akalla mutane 10,217 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a jihohin Benue, Niger, Katsina, Kebbi, Plateau, Sokoto da Zamfara.
Amnesty international ta ce jihar Benue ce ta fi yawan adadin wadanda aka kashe, sai jihar Plateau da aka kashe mutane 2,630.
Wannan na zuwa ne cikin shekaru uku na wa’adi guda a mulkin Bola Ahmed Tinubu tare da alkawarin inganta tsaro. Sai dai a maimakon samun sauki, al’amura sun kara tabarbarewa, yayin da hukumomi ke ci gaba da gaza kare hakkin rayuwa, lafiyar mutane, ‘yanci da tsaron dubban al’umma a fadin Najeriya.
A cikin shekaru biyu na farko na gwamnatin ta Tinubu, Amnesty ta ce an samu ɓullar wasu sabbin kungiyoyin ‘yan bindiga m, ciki har da Lakurawa a jihohin Sokoto da Kebbi, da kuma Mamuda a jihar Kwara.
Haka kuma, ‘yan bindiga sun kori daruruwan kauyuka daga gidajensu a jihohin Benue, Borno, Katsina, Sokoto, Plateau da Zamfara.
Yawaitar hare-haren na barazana da jefa kasar cikin babbar matsala, kuma mafi yawan mutanen da suka rasa matsugunansu a jihohin Plateau da Katsina sun shaida wa Amnesty International cewa dole ne su koma bara domin samun abin da za su ci a kullum.
A gundumar Dangulbi ta jihar Zamfara, manoma na kallon amfanin dankalin Hausa da suka noma yana rubewa, saboda ‘yan bindiga sun hana su kai shi kasuwar da ke kusa.
Amnesty international ta ce a karkashin dokokin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, hukumomi suna da alhakin kare rayukan jama’a da tabbatar da ganin an hukunta wadanda ake zargi da aikata wadannan kashe-kashen, tare da bai wa wadanda lamarin ya shafa damar samun adalci da diyya mai inganci.
Sai dai Amnesty International ta ce hukumomin Najeriya na ci gaba da gaza cika wadannan wajibai.
