DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeLabaraiKada ku siya min kyauta a bikin ranar haihuwata, ku yi sadaka...

Kada ku siya min kyauta a bikin ranar haihuwata, ku yi sadaka da kuɗin – Kashim Shettima

Mataimakin shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya buƙaci ’yan Nijeriya da kada su kashe kuɗi wajen sayen masa kyaututtuka ko shirya bukukuwan murnar cikarsa shekara 60, inda ya ce a maimakon haka, a bayar da kuɗin ga masu buƙata da ƙungiyoyin agaji.

Gidan talabijin na TVC News ya ruwaito Shettima ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a daren Talata, gabanin ranar haihuwarsa da ta kasance Laraba, 2 ga Satumba, 2026.

Ya ce cikar shekara 60 ta ƙara masa ƙwarin gwiwar yin watsi da al’adar karɓar kyaututtukan ranar haihuwa da kuma kashe kuɗaɗe wajen gudanar da bukukuwa domin girmama shi.

A cewarsa, wannan babban mataki na rayuwa ya kamata ya zama lokacin yin tunani, nuna godiya da kuma taimakon jama’a, maimakon tara dukiya ko kayan more rayuwa.

Mataimakin shugaban ƙasar ya shawarci abokai, magoya baya, abokan hulɗa da sauran masu fatan alheri da su karkatar da duk wani kuɗin da za su kashe wajen yi masa kyauta zuwa ga ƙungiyar agaji, wani muhimmin aikin jinƙai ko kuma wani mutum da ke cikin buƙata.

Shettima ya ce duk wani mutum da zai taimaka wa wani a Nijeriya a ranar haihuwarsa, zai zama kamar ya kunna masa kyandir na murna, yana mai cewa irin wannan aiki ne zai fi zama abin tunawa da shi.

Ya kuma nemi ’yan Nijeriya da su yi masa addu’a tare da yi wa ƙasar addu’ar samun zaman lafiya, ci gaba, shugabanci nagari da kuma damar amfani da albarkatun da Allah Ya bai wa Nijeriya.

Mataimakin shugaban ƙasar ya nuna godiya ga ’yan Nijeriya bisa fatan alheri, abota da addu’o’in da suka ci gaba da yi masa tsawon shekaru, yana mai cewa babu wanda zai iya kaiwa wani babban matsayi a rayuwa ta hanyar ƙoƙarinsa shi kaɗai.

Ya ƙara da cewa wajibi ne ’yan Nijeriya su riƙa nuna tausayi da taimakon juna, musamman ga mutanen da ba za su taɓa samun damar mayar da irin wannan alheri ba.

Shettima ya kuma bayyana matasan Nijeriya, bambancin al’adu, ƙwazo wajen kasuwanci da kuma damar da ’yan ƙasar ke da ita ta zauna tare duk da bambance-bambancen da ke tsakaninsu, a matsayin wasu daga cikin manyan kadarorin ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata