DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 22, 2026
HomeLabaraiƁata-gari sun lalata manyan turakun lantarki shida a Nasarawa

Ɓata-gari sun lalata manyan turakun lantarki shida a Nasarawa

Kamfanin Kula da Rarraba Wutar Lantarki na Nijeriya (TCN) ya ce wasu ɓarayi sun lalata manyan turakun isar da wutar lantarki guda shida a kan layin Apir-Lafia da ke jihar Nasarawa, lamarin da ya haddasa tangarɗa mai tsanani ga samar da wuta a wasu yankuna.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa Babbar Manajar Hulɗa da Jama’a ta TCN, Misis Ndidi Mbah, ta bayyana a ranar Laraba cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:15 na dare ranar 30 ga Mayu yayin da ake ruwan sama mai ƙarfi.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa bayan layin ya samu matsala, injiniyoyin TCN sun yi ƙoƙarin dawo da wutar ta hanyar sake kunna layin na biyu, amma hakan bai yi nasara ba. Daga bisani binciken da aka gudanar a kan layin ya gano cewa an lalata muhimman sassan turaku daga T125 zuwa T130, abin da ya tabbatar da cewa an yi aikin ɓarna ne da gangan.

A sakamakon haka, layukan isar da wuta na Apir-Lafia 330kV na ɗaya da na biyu sun daina aiki gaba ɗaya har sai an sake gina turakun da aka lalata. TCN ta ce ta tura injiniyoyinta zuwa wurin domin tantance girman ɓarnar da kuma kayan da za a buƙata domin fara aikin gyara.

Kamfanin ya ce a halin yanzu ana samar da wuta ga tashar Lafia ta hanyar layin Lafia-Jos a matsayin matakin wucin gadi domin rage tasirin matsalar ga kwastomomin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) da na Jos (JEDC).

TCN ta yi Allah-wadai da ci gaba da lalata kayayyakin lantarki, tana mai cewa irin waɗannan ayyuka na janyo hasarar biliyoyin kuɗaɗen da aka zuba a fannin wutar lantarki tare da kawo cikas ga samar da ingantacciyar wuta ga al’umma.

Kamfanin ya yi kira ga al’ummomin da ke kusa da turakun lantarki da sauran jama’a su kasance masu sa ido tare da kai rahoton duk wani motsi da ake zargi ga hukumomin tsaro ko ofisoshin TCN mafi kusa.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata