DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeSiyasaMalaman Musulunci 500 sun amince da tazarcen Tinubu a Jigawa – Ibrahim...

Malaman Musulunci 500 sun amince da tazarcen Tinubu a Jigawa – Ibrahim Masari

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa da sauran al’amura, Ibrahim Masari, ya ce sama da malaman addinin musulunci da shugabannin addini 500 sun amince da sake zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Jaridar Punch ta ruwaito Masari ya bayyana hakan ne bayan halartar taron northern muslim intellectual forum da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, inda aka tattaro malamai, masana, shugabannin addini da sauran masu ruwa da tsaki daga jihohin arewa 19 da babban birnin tarayya, Abuja.

A cewar sanarwar da ofishin yaɗa labaran Masari ya fitar, taron ya samu halartar kusan mutane 500 da suka haɗa da shehunai, limamai, alarammomi da masu wa’azi. Mahalarta taron sun tattauna kan matsalolin tsaro, tattalin arziki da ci gaban yankin arewacin Nijeriya.

Sanarwar ta ce mahalarta taron sun nuna gamsuwa da matakan da gwamnatin Tinubu ke ɗauka wajen magance matsalolin da ke addabar arewa, musamman a fannin tsaro. Sun kuma bayyana cewa an samu ci gaba a wasu fannoni na tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa da sauran ayyukan ci gaba.

Bayan tattaunawar, mahalarta taron sun amince da ƙudurin mara wa Tinubu baya domin ya sake tsayawa takara a zaɓen 2027. Sun kuma bayyana ƙwarin gwiwa kan alkiblar da gwamnatinsa ta ɗauka wajen aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki, bunƙasa ababen more rayuwa da inganta tsaro.

Bugu da ƙari, taron ya zartar da ƙuri’ar amincewa da shugabancin Tinubu, tare da kira ga ‘yan Nijeriya, musamman mazauna yankin arewa, da su mara masa baya a zaɓen 2027 tare da zaɓen sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC.

Daga cikin manyan jami’an gwamnati da suka halarci taron akwai gwamnan Jigawa, Umar Namadi; gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf; gwamnan Yobe, Mai Mala Buni; gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu; da gwamnan Kaduna, Uba Sani.

Sauran sun haɗa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, da ministan gidaje da raya birane, Muttaka Darma da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata