Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Peter Obi, ya soki wasu malaman addini bisa zargin yi wa ’yan siyasar da ya kira masu aikata laifuka addu’a, yana mai cewa hakan na daga cikin alamun barazanar da Nijeriya ke fuskanta.
Obi ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin taron tattaunawa kan dimokuraɗiyya na shekarar 2026 da gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya a Bauchi.
Tsohon gwamnan jihar Anambran ya kuma soki tsarin shari’a da na zaɓe a ƙasar, yana mai cewa wasu sauye-sauyen da aka samu sun raunana muhimman ginshiƙan dimokuraɗiyya.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Obi ya ce halin da ake ciki ya nuna cewa akwai babbar matsala, musamman yadda wasu shugabannin addini ke yi wa ’yan siyasar da ake zargi da aikata laifuka addu’ar samun albarka a al’amuran su.
Obi ya kuma taɓo batun ƙalubalen da ya fuskanta a kotu bayan zaɓen da ya gabata, inda ya ce ya kwashe shekaru uku yana ƙalubalantar sakamakon zaɓen.
Ya bayyana cewa alkalai biyar da bai taɓa haɗuwa da su ba sun taɓa yanke hukunci da ya goyi bayan ƙalubalensa, yana mai cewa irin wannan yanayi ba zai yiwu a Nijeriya ta yau ba.
Haka kuma, Obi ya zargi ‘yan majalisa da raunana dokokin zaɓe, inda ya yi ikirarin cewa an cire laifin jabun takardun karatu daga cikin wasu laifukan da suka shafi harkokin zaɓe.
Ya kuma soki yadda wasu lauyoyi ke kare shari’o’in da suka shafi zargin takardun bogi, yana mai cewa hakan na ƙara nuna yadda ake raunana tsarin tabbatar da sahihancin zaɓe a kasar.
A cewarsa, Nijeriya na buƙatar sauya wannan yanayi domin illolin cin zarafin tsarin dimokuraɗiyya da ake bari a yau na iya dawo wa kan al’ummomi da kuma ’yan ƙasar a nan gaba.
