DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 29, 2026
HomeLabaraiShettima ya dawo Nijeriya bayan halartar taron MDD

Shettima ya dawo Nijeriya bayan halartar taron MDD

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima, ya dawo kasar bayan ya jagoranci tawaga mai karfi zuwa babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 da aka gudanar a birnin New York na ƙasar Amurka.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Shettima ya koma Nijeriya ne a ranar Litinin, bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi umarnin jagorantar tawagar ƙasar zuwa taron Majalisar Ɗinkin Duniya na bana.

Mataimakin shugaban kasar ya bar Abuja ne ranar 20 ga Satumba domin wakiltar shugaba Tinubu a babban taron da ke haɗa shugabannin ƙasashe daban-daban na duniya.

A cewar sanarwar da babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban sasa kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha, ya fitar, Shettima ya gabatar da jawabin Nijeriya a zaman muhawarar babban taron.

A yayin taron, Nijeriya ta sake jaddada buƙatar yin garambawul ga kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya domin samar da tsarin da zai bai wa kasashe damar wakiltar yankuna daban-daban.

Nijeriya ta kuma yi kira da a samu wakilcin Afirka na dindindin a kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya, tare da neman ingantaccen tsarin samar da kuɗaɗen ci gaba a duniya.

Haka kuma, Nijeriya ta buƙaci ƙasashen duniya su ƙara tallafa wa ƙasashen da ke fuskantar matsalolin sauyin yanayi, tare da ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashe wajen tunkarar ƙalubalen duniya.

A wani taro na manyan jami’ai kan dabarun sarrafa albarkatun ma’adinan Afirka, Shugaba Tinubu ya buƙaci ƙasashen Afirka su daina dogaro da fitar da ma’adinai kawai.

A cewarsa, ya kamata ƙasashen nahiyar su mayar da hankali kan sarrafa ma’adinai a cikin gida, masana’antu da ƙara darajar kayayyakin da ake samu daga albarkatun ƙasa.

Shettima ya kuma halarci wani babban taro kan samar da kuɗaɗen ilimi wanda Nijeriya da Italiya suka shirya tare.

A yayin taron, ya sake jaddada aniyar gwamnatin tarayya na ƙara zuba jari a fannin ilimi, yana mai bayyana ilimi a matsayin muhimmin jari wajen bunƙasa ƙwarewar ’yan ƙasa da tattalin arzikin ƙasa.

Mataimakin shugaban kasar ya kuma nuna goyon bayan Nijeriya ga shirin Global Partnership for Education na neman samar da dala biliyan biyar domin tallafa wa harkokin ilimi a ƙasashe daban-daban.

A yayin ziyarar, Shettima ya kuma gana da ’yan Nijeriya da ke zaune a ƙasashen waje, inda ya bayyana muhimmancin gudunmawar da suke bayarwa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa ta hanyar zuba jari, ƙwarewa da sauran hanyoyi.

Sanarwar ta ce mataimakin shugaban kasar ya kuma gana da sabbin shugabannin lungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS), da mataimakiyar Sakatare-Janar ta majalisar ɗinkin duniya, Amina Mohammed.

Tattaunawar da aka gudanar a yayin ganawar ta shafi batutuwan samar da kuɗaɗen ci gaba, haɗin kan yankin, tattalin arziki, fasaha, zaman lafiya da tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata