DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeWasanniZidane ya sanya hannu kan yarjejeniyar zama kocin Faransa har zuwa 2030

Zidane ya sanya hannu kan yarjejeniyar zama kocin Faransa har zuwa 2030

Shahararren tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafar Faransa, Zinedine Zidane, ya rattaba hannu kan yarjejeniya domin zama sabon kocin tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar Faransa har zuwa watan Yunin shekarar 2030, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Rahoton ya fito ne daga mashahurin masanin harkokin musayar ‘yan wasa, Fabrizio Romano, wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata cewa za a gabatar da tsohon kocin Real Madrid a hukumance cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

Fabrizio ya ce, “Zinedine Zidane ya sanya hannu a matsayin sabon kocin Faransa har zuwa watan Yunin 2030, an tabbatar da yarjejeniyar, kuma za a gabatar da shi a hukumance cikin kwanaki masu zuwa.”

A cewarsa, Zidane zai jagoranci tawagar Faransa a gasar UEFA Nations League ta 2027, Euro 2028, da kuma Gasar Kofin Duniya ta FIFA ta 2030.

Zidane mai shekaru 54 bai sake aikin horaswa ba tun bayan da ya bar Real Madrid a shekarar 2021, bayan wa’adi na biyu da ya yi a kulob ɗin.

A lokacin da yake jagorantar Real Madrid, Zidane ya lashe kofunan Zakarun Turai uku a jere tsakanin shekarun 2016 zuwa 2018, sannan ya lashe La Liga sau biyu tare da wasu manyan kofuna na cikin gida da na duniya.

Tsohon gwarzon da ya taimaka wa Faransa lashe Kofin Duniya na 1998 ya daɗe ana danganta shi da kujerar horas da tawagar ƙasar, kuma mutane da dama sun ɗauke shi a matsayin wanda zai gaji Didier Deschamps, wanda ya jagoranci Faransa tun shekarar 2012.

Ana sa ran Deschamps zai bar mukaminsa bayan kammala Kofin Duniya na 2026, yayin da Zidane ya taɓa bayyana a baya cewa yana da burin horas da tawagar ƙasar Faransa.

Sai dai zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumar kwallon kafar Faransa ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance da ke tabbatar da naɗin Zidane ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata