DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeSiyasaAtiku ya taya Adeleke murnar sake lashe zaɓen Osun

Atiku ya taya Adeleke murnar sake lashe zaɓen Osun

Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya taya Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, murnar sake lashe zaɓen gwamnan jihar.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Atiku ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, inda ya ce nasarar Adeleke ta nuna zaɓin da al’ummar Osun suka yi a rumfunan zaɓe.

Atiku ya ce sakamakon zaɓen ya nuna cewa al’ummar jihar sun bayyana ra’ayinsu a fili ta hanyar ƙuri’un da suka kaɗa.

Ya kuma yaba wa jama’ar Osun bisa yadda suka yi zaɓen cikin lumana, yana mai cewa irin wannan hali na taimakawa wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya a ƙasar.

Tsohon mataimakin Shugaban Nijeriyar ya kuma yi wa Adeleke fatan samun nasara a wa’adinsa na biyu, tare da ci gaba da yi wa al’ummar jihar hidima.

Adeleke, wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar Accord, hukumar zaben Nijeriya INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen ranar Lahadi.

Ya samu ƙuri’u 511,067, inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na jam’iyyar APC, wanda ya samu ƙuri’u 444,815.

Nasarar ta bai wa Adeleke damar sake komawa kan kujerar gwamnan Osun domin wa’adin mulki na biyu, bayan da ya samu rinjaye a zaɓen da aka gudanar ranar Asabar.

A cikin sakonsa, Atiku ya kuma buƙaci al’ummar Osun su ci gaba da bai wa gwamnati goyon baya wajen gudanar da ayyukan da za su amfani jihar.

Ya ce nasarar zaɓen na da muhimmanci wajen tabbatar da cewa muradin jama’a na samun damar zaɓar shugabanninsu cikin ’yanci da lumana ya ci gaba da tabbata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata