DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 29, 2026
HomeLabaraiKotu za ta saurari buƙatar Atiku na gyara ƙarar da ya shigar...

Kotu za ta saurari buƙatar Atiku na gyara ƙarar da ya shigar kan Tinubu da APC

Babbar Kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 13 ga Oktoba, 2026 domin sauraron buƙatar tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, na neman gyara ƙarar da ya shigar kan Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito mai shari’a Inyang Ekwo ne ya sanya ranar domin bai wa ɓangarorin da abin ya shafa damar kammala da daidaita takardun shari’arsu kafin fara sauraron buƙatar.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa an ɗage sauraron buƙatar ne bayan lauyan Atiku da ADC ya bayyana cewa har yanzu bai samu takardar da tawagar lauyoyin Shugaba Tinubu ta shigar kan buƙatar gyaran ƙarar ba.

A zaman kotun na ranar Litinin, Joseph Silas, wanda ya wakilci Atiku da ADC, ya ce ya samu martanin sauran waɗanda ake ƙara, amma bai samu takardar amsar Shugaba Tinubu ba.

Sai dai babban Lauyan Shugaba Tinubu, Cif Wole Olanipekun, SAN, ya shaida wa kotun cewa an miƙa wa lauyoyin masu ƙara takardar amsar ne tun ranar 24 ga Satumba, kuma ofishin lauyoyin Atiku ya amince da karɓarta.

Mai shari’a Ekwo ya tabbatar da shaidar miƙa takardar da Olanipekun ya gabatar wa kotu, kafin ya ɗage batun zuwa ranar 13 ga Oktoba domin sauraron buƙatar gyaran ƙarar.

A cikin ƙarar, Atiku da jam’iyyar ADC sun roƙi kotun da ta hana Shugaba Tinubu da APC shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2027, bisa wasu ƙorafe-ƙorafe da suka shafi takardar shaidar kammala hidimar ƙasa ta NYSC da aka gabatar wa INEC.

Masu ƙarar sun yi zargin cewa an gabatar wa hukumar INEC takardar NYSC da suka ce ba ingantacciya ba ce, inda suka nemi kotu ta umarci INEC ta cire sunan Shugaba Tinubu da na APC daga jerin waɗanda za su shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1888/2026, da Atiku da ADC suka shigar da Shugaba Tinubu, APC da INEC a matsayin waɗanda ake ƙara.

Sai dai Shugaba Tinubu da APC sun musanta zargin, inda a cikin takardar amsa da suka gabatar ranar 9 ga Satumba, suka roƙi kotun da ta yi watsi da ƙarar.

Ta hannun daraktan sashen Shari’a na APC, Sanusi Samaila, ɓangarorin biyu sun ce ba su gabatar da wata takardar Form CF001 ga INEC ba kamar yadda masu ƙarar suka yi zargin.

Sun kuma ce hukumar NYSC ba ta taɓa musanta cewa ita ce ta bayar da takardar shaidar kammala hidimar ƙasa da ake magana a kai ba.

Tinubu da APC sun kuma yi hujjar cewa idan ana zargin takarda ta ƙirƙira ce, ana buƙatar hukuma ko cibiyar da ake cewa ita ce ta fitar da takardar ta bayyana cewa ba ita ta bayar da ita ba.

A nata ɓangaren, INEC ma ta kalubalanci ƙarar, inda Lauyanta, Dr Alex Izinyon, SAN, ya shigar da ƙin amincewa da ƙarar a ranar 7 ga Satumba.

INEC ta ce ƙarar tana da matsalolin shari’a da suka haɗa da wucewar lokacin shigar da ƙara, rashin cikakken haƙƙin shigar da ƙarar, rashin gamsasshen dalilin ƙara da kuma zargin amfani da tsarin kotu ba daidai ba.

Hukumar ta kuma yi zargin cewa masu ƙarar ba su cika wasu buƙatun da dokokin kotu suka shimfiɗa ba, musamman batun rubutacciyar shaida da ake buƙata a shari’un da suka shafi zaɓe.

Bayan haka, Atiku da ADC sun shigar da wata buƙata a ranar 10 ga Satumba suna neman izinin kotu domin gyara ƙarar tasu.

A cikin buƙatar, sun ce bayan sun shigar da ƙarar a ranar 14 ga Agusta, sun gano wasu kura-kurai da suka shafi sunayen wasu fom ɗin INEC da aka ambata a cikin takardunsu.

Sun bayyana cewa an kira wani fom da sunan CF001, alhali suna son gyara shi zuwa fom ɗin da suke cewa shi ne ya dace da sabon tsarin takardun INEC, tare da ƙara wasu bayanai da suka shafi zargin da suka gabatar.

Atiku da ADC sun kuma ce suna son ƙara rubuta shaida daga Atiku tare da gabatar da ƙarin kwafi masu bayyana na wasu takardun da aka ambata a cikin ƙarar.

Sun ce gyaran da suke nema ba zai ƙara wata sabuwar matsala ko wata sabuwar buƙata ba, sai dai ya taimaka wajen gyara kura-kurai da kuma gabatar da cikakkun bayanan da suke ganin ya kamata kotu ta duba.

Sai dai Shugaba Tinubu ya yi adawa da wannan buƙata, inda a cikin takardar da aka shigar ranar 24 ga Satumba, ya ce gyaran da Atiku ke nema ya wuce gyaran kura-kuran rubutu kawai.

A cewar Moses Adoga, wani jami’in tallafa wa harkokin shari’a a ofishin lauyan Tinubu, gyaran da ake nema zai sauya wasu daga cikin abubuwan da aka gabatar a ƙarar ta asali, ciki har da tambayoyin da ake son kotu ta yanke hukunci a kansu da kuma wasu daga cikin buƙatun masu ƙara.

Ya kuma yi zargin cewa Atiku da ADC suna son ƙara wasu sabbin takardu da sakin layi a cikin takardun shari’ar, lamarin da ya ce zai iya sauya yadda aka gabatar da ƙarar tun farko.

Adoga ya kuma yi hujjar cewa ƙarar da aka shigar ta samu matsalar wa’adin da doka ta tanada, yana mai cewa ba za a iya amfani da gyaran ƙara wajen magance matsalar da ta shafi hurumin kotu bayan ƙarewar lokacin da kundin tsarin mulki ya tanada ba.

APC ma ta nuna adawa da buƙatar Atiku da ADC na neman gyara ƙarar, yayin da INEC ta gabatar da nata martanin kan wannan buƙata.

A cewar INEC, gyaran da ake nema zai iya kawo sabon dalilin ƙara ko kuma sauya wasu muhimman abubuwan da aka gina ƙarar a kansu bayan ƙarewar lokacin da doka ta tanada na shigar da ƙarar da ta shafi zaɓe.

Hukumar ta kuma yi hujjar cewa bai kamata a yi amfani da gyaran ƙara wajen magance matsalar hurumin kotu ko kuma kawo wata sabuwar ƙara bayan wa’adin da kundin tsarin mulki ya kayyade ba.

Saboda haka, batun da kotun za ta fara saurara ranar 13 ga Oktoba shi ne buƙatar Atiku da ADC na neman izinin gyara takardun ƙarar da suka shigar kan Shugaba Tinubu, APC da INEC.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata