Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya buƙaci mazauna babban birnin su yi amfani da zaɓen 2027 wajen zaɓar shugabannin da za su ci gaba da faɗaɗa ayyukan raya ƙasa da ake gudanarwa a Abuja.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Wike ya yi wannan kira ne a cikin saƙon taya murna da ya aika wa mazauna birnin a ranar Alhamis, yayin da Nijeriya ke bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai.
Ministan ya ce gwamnatin FCTA ta zuba jari sosai a ayyukan more rayuwa, ciki har da gina tituna da inganta harkokin sufuri, domin kai ci gaba zuwa yankunan karkara da ke wajen tsakiyar birnin Abuja.
Ya ce an sauya tsarin hanyoyin Abuja daga tsakiyar birni zuwa wasu yankunan karkara, inda aka samar da magudanan ruwa da fitilun hasken titi. A cewarsa, ayyukan na da nufin sauƙaƙa zirga-zirga da kuma taimakawa wajen inganta tsaro.
Wike ya kuma bayyana cewa an gina tashoshin motocin haya na zamani a Abuja Municipal Area Council (AMAC), tare da shirin faɗaɗa irin waɗannan ayyuka zuwa Kuje, Bwari da Gwagwalada.
Game da kiwon lafiya da ilimi, ya ce gwamnatin FCT na ƙoƙarin inganta ayyukan waɗannan fannoni a dukkan ƙananan hukumomin yankin guda shida, yana mai cewa al’umma mai lafiya da ilimi na da muhimmiyar rawa wajen samun ci gaba mai ɗorewa.
Dangane da zaɓen 2027, Wike ya buƙaci mazauna Abuja su zaɓi shugabannin da, a cewarsa, ke da hangen nesa da ƙwarewar ci gaba da ayyukan raya ƙasa. Ya kuma yi kira ga jama’a da su kare kayayyakin gwamnati daga lalacewa tare da ci gaba da zaman lafiya, haƙuri da haɗin kai a tsakanin al’ummar Abuja.
