DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeLabaraiNDC ta gargadi ƴan takararta su guji tashin hankali da kalaman batanci...

NDC ta gargadi ƴan takararta su guji tashin hankali da kalaman batanci a yaƙin neman zaɓen 2027

Jam’iyyar NDC a Nijeriya ta gargadi ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi, da sauran ƴan takararta na kujerun gwamnoni da majalisar dokokin kasar, da su tabbatar da cewa yakin neman zabensu na 2027 ya kasance cikin zaman lafiya kuma bisa batutuwa masu muhimmanci.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa jam’iyyar ta kuma umurci ƴan takararta da su fara tuntubar jama’a da masu ruwa da tsaki tare da fara ayyukan yakin neman zaɓe a faɗin ƙasar.

A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Osa Director, ya fitar a Abuja, NDC ta ce ya kamata ƴan takararta su gudanar da tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma al’ummomin da suke neman wakilta.

Ya ce ƴan takarar jam’iyyar, musamman na shugaban ƙasa da majalisar dokoki ta kasa, su fara tuntuba, wayar da kan jama’a da ganawa da masu zaɓe, tare da bayyana manufofi da akidar jam’iyyar.

NDC ta jaddada cewa duk wani yakin neman zaɓe na jam’iyyar dole ne ya kasance bisa tsarin manufofi, ba tare da tashin hankali ko amfani da kalaman batanci ba.

Sakataren ya ce “tashin hankali ba shida wani gurbi a jam’iyyar”, inda ya buƙaci ƴan takara da magoya bayansu su kiyaye dokokin yaƙin neman zaɓe tare da mutunta sauran ƴan takara.

Sai dai jam’iyyar ta ce har yanzu ana kammala wasu matakan gudanarwa kafin a fara amfani da sabon tambarinta a hukumance.

Saboda haka, NDC ta umarci ƴan takararta da mambobinta su ci gaba da amfani da tsohon tambarin jam’iyyar, wanda kuma yake ɗauke da alamar ɗaga yatsu biyu ta nasara, har sai an kammala dukkanin matakan da suka shafi sauya tambarin tare da INEC.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata