DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeKetareNijeriya ta jajanta wa China kan ambaliyar ruwa

Nijeriya ta jajanta wa China kan ambaliyar ruwa

Gwamnatin Nijeriya ta jajanta wa ƙasar China kan ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa da ta afku a yankin kan iyakar China da Nepal a ranar 26 ga Agusta, 2026.

A cikin wata sanarwa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya, Oluwafemi Adeniyi, ya ce iftila’in ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata daruruwan wasu, baya ga lalata kadarori da dama a Gyirong County da ke Tibet.

Nijeriya ta kuma jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu, ciki har da Sinawa da ’yan Nepal da kuma wasu ’yan ƙasashen waje daga Australia, Indiya, Malaysia, Birtaniya da Amurka.

Gwamnatin Nijeriya ta yaba wa Shugaban China, Xi Jinping, da ƙungiyoyin ceto na ƙasar bisa gaggauta ɗaukar mataki da kuma ci gaba da ayyukan jinƙai domin tallafa wa waɗanda iftila’in ya shafa.

Gwamnatin ta ce tana tare da al’ummar China a wannan lokaci na jarrabawa, tare da addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka mutu, Ya ba waɗanda suka jikkata lafiya, sannan Ya tallafa wa mutanen da suka rasa matsugunansu yayin da ake ci gaba da aikin farfaɗowa daga bala’in.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata