DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeBabban Labari Nijeriya ta ci gaba da rike matsayin kasar da ta fi kowace...

Nijeriya ta ci gaba da rike matsayin kasar da ta fi kowace kasa yawan al’umma a Afirka

Nijeriya ta ci gaba da kasancewa ƙasar da ta fi kowace ƙasa yawan al’umma a Afirka, inda aka kiyasta yawan jama’arta da mutum miliyan 242.4 a shekarar 2026.

Bisa sabon hasashen Worldometer da jaridar Punch ta ruwaito, wannan adadi ya tabbatar da Nijeriya a matsayi na farko a jerin ƙasashen Afirka mafi yawan al’umma.

Habasha ce ke matsayi na biyu da yawan jama’a miliyan 138.9, yayin da Masar ke matsayi na uku da mutum miliyan 120.1.

Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ce ke matsayi na huɗu da miliyan 116.5, sai Tanzaniya da ke matsayi na biyar da miliyan 72.6.

Afirka ta Kudu ce ke matsayi na shida da miliyan 65.5, sai Kenya mai miliyan 58.6, Sudan mai miliyan 53.3 da Uganda mai miliyan 52.8.

Aljeriya ce ta kammala jerin ƙasashe 10 mafi yawan al’umma a Afirka, inda aka kiyasta yawan jama’arta da mutum miliyan 48.

Rahoton ya ce alkaluman Nijeriya hasashe ne, domin ƙidayar jama’a ta ƙarshe da aka gudanar a ƙasar ita ce ta shekarar 2006, lokacin da yawan jama’ar ƙasar ya kai miliyan 140.4.

Ana sa ran yawan jama’ar Afirka zai haura biliyan 2.5 nan da shekarar 2050, sakamakon yawan matasa, ƙaruwar haihuwa da kuma ingantuwar kiwon lafiya.

Rahoton ya bayyana cewa ci gaba da ƙaruwa da yawan jama’ar Nijeriya na iya yin tasiri sosai kan kasuwanci, saka hannun jari, samar da ayyukan yi da ci gaban tattalin arzikin nahiyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata