DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, September 23, 2026
HomeLabaraiTinubu ya ƙaddamar da horas da matasa 5,000 kan sanya mitar lantarki

Tinubu ya ƙaddamar da horas da matasa 5,000 kan sanya mitar lantarki

Shugaba Bola Tinubu ya sanar da ƙaddamar da shirin horas da matasa 5,000 a matsayin masu sanya da gyaran mitar lantarki ƙarƙashin Shirin Presidential Metering Initiative (PMI).

Shugaban ya ce shirin, mai suna The Power Force, na da burin samar da ayyukan yi, rage gibin mitoci da kuma inganta samar da wutar lantarki a Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya ce shirin wani ɓangare ne na manufofin gwamnatin sa na Renewed Hope domin buɗe ƙarin damammakin aiki ga matasa.

Ya bayyana cewa mahalarta shirin za su samu horo kan ƙwarewar girka da gyaran mitoci, tare da samun damar aiki a fannin lantarki.

Tinubu ya ce shirin zai kasance a buɗe ga waɗanda suka kammala karatun sakandare, yayin da aka ware gurbi na musamman ga masu yi wa ƙasa hidima (NYSC).

Ya ƙara da cewa amfani da mitoci zai taimaka wajen kawo ƙarshen tsarin ƙiyasta kuɗin wutar lantarki da kuma kare haƙƙin masu amfani da wutar.

A cewarsa, idan gidaje da kamfanoni suna da mitoci, za su biya kuɗin wutar da suka yi amfani da ita kawai, yayin da kamfanonin rarraba wuta za su inganta ayyukansu cikin adalci da gaskiya.

Tinubu ya ce ya umarci PMI ta haɗa kai da Ma’aikatar Matasa ta Tarayya da Cibiyar Horar da Ma’aikatan Lantarki ta Nijeriya (NAPTIN) da sauran masu ruwa da tsaki domin fara shirin cikin kwanaki 30 masu zuwa.

Ya kuma buƙaci matasan da suka cancanta su nemi shiga shirin, yana mai cewa hakan zai ba su sana’a mai amfani tare da taimakawa wajen kawo ƙarshen tsarin ƙiyasta kuɗin wutar lantarki a ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata