DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeSiyasaZan tsige duk Ciyaman ɗin da APC ta yi rashin nasara a...

Zan tsige duk Ciyaman ɗin da APC ta yi rashin nasara a karamar hukumarsa – Gwamnan Ebonyi

Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya yi barazanar maye gurbin duk wani shugaban ƙaramar hukumar da ya kasa tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a ƙaramar hukumarsa a zaɓen 2027.

Nwifuru ya bayyana hakan ne a Abakaliki, babban birnin jihar, yayin ƙaddamar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi 13 da mataimakansu, inda ya ce ba zai bar shugabannin ƙananan hukumomi su yi sakaci wajen ganin APC ta samu nasara ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Gwamnan ya ce duk shugaban ƙaramar hukumar da ya kasa lashe ƙaramar hukumarsa a zaɓen 2027 za a cire shi daga mukaminsa, sannan a maye gurbinsa da wani kansila.

Nwifuru ya kuma buƙaci shugabannin ƙananan hukumomin su yi duk mai yiwuwa domin APC ta samu kashi 100 cikin 100 na ƙuri’un da ake sa ran samu a jihar a zaɓen 2027, tare da gargadin su da kada su bari jam’iyyun adawa su samu damar ƙarfafa matsayinsu a yankunansu.

Gwamnan ya kuma shawarci mataimakan shugabannin ƙananan hukumomin da su kasance masu aiki tare da shugabanninsu, yana mai cewa bai kamata su bari jita-jita ko shawarwarin abokai su lalata kyakkyawar alaƙarsu da shugabannin ba.

A nasa jawabin, shugaban ƙaramar hukumar Afikpo, Timothy Nwachi, wanda ya yi magana a madadin takwarorinsa, ya gode wa gwamnan da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC bisa damar da aka ba su ta yi wa al’umma hidima.

Inda aka ruwaito ya yi alkawarin cewa za su tabbatar da APC ta samu gagarumar nasara a zaɓen 2027 da ke tafe a watan Janairun sabuwar shekara.

Sabbin shugabannin sun haɗa da Osborne Umahi, ɗan Ministan Ayyuka, David Umahi, da Chidi Nwode, ɗan’uwan matar Gwamna Nwifuru da dai sauransu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata