Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya sake saka dokar hana fita ta awa 24 a karamar hukumar Lamurde, sakamakon sake barkewar hare-hare da tashin hankali ga wasu al’ummomin yankin.
Mai magana da yawun gwamnan, Humwashi Wonosikou, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a birnin Yola.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnati ta dauki wannan mataki ne bayan sake samun rikice-rikice da suka haddasa asarar rayukan wasu mazauna yankin.
