Saturday, March 21, 2026
HomeWasanniJoan Laporta ne ya hana Lionel Messi dawowa Barcelona don kauce wa...

Joan Laporta ne ya hana Lionel Messi dawowa Barcelona don kauce wa rikicin shugabanci — Xavi Hernández

Tsohon kocin kungiyar Barcelona, Xavi Hernández, ya bayyana cewa shugaban kulob din a wancan lokaci, Joan Laporta, ne ya hana dawowar fitaccen dan wasa Lionel Messi kungiyar a shekarar 2023.

Xavi ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar La Vanguardia, inda ya ce bayan Messi ya lashe 2022 gasar kofin duniya, ya tuntube shi a watan Janairun 2023 kuma ya nuna sha’awar komawa Barcelona.

Google search engine

A cewarsa, kungiyar ta riga ta samu amincewar La Liga ta domin kammala cinikin dawowar Messi, amma daga baya shugaban kulob din ya dakatar da shirin.

Ya ce Laporta ya gaya mai kai tsaye cewa idan Messi ya dawo, zai iya haifar da rikicin iko a kulob din, kuma ba zai bari hakan ta faru ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata