Saturday, March 21, 2026
HomeLabaraiMajalisar dokokin jihar Rivers sun fara tantance sunaye sabbin kwamishinoni

Majalisar dokokin jihar Rivers sun fara tantance sunaye sabbin kwamishinoni

‘Yan majalisar dokokin jihar Rivers sun fara tantance sunayen mutanen da gwamnan jihar Siminalayi Fubara ya gabatar domin nada su a matsayin kwamishinoni.

Rahotanni sun nuna cewa mutum tara ne aka raka zuwa majalisar da misalin karfe 10 na safe a ranar Litinin domin fara tantance su.

Google search engine

Mutanen da aka gabatar sun hada da Datonye Alasia, Tonye Bellgam, Temple Nwofor, Peters Nwagor, Charity Deemua, Tamuno Williams, Lekue Kenneth, Otonye TKD Amachree, da kuma Amairigha Hart.

A cikin wani bidiyo da tashar Arise TV ta watsa, an ga kowane daga cikin wadanda aka gabatar yana hawa mumbari yana gabatar da kansa tare da amsa tambayoyin ‘yan majalisar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata