Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar da cewa dokar ta ɓaci da aka ayyana kan tsaro ta zama tana aiki a zahiri, ba magana kawai ba.
Ndume ya bayyana hakan ne bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai garin Ngoshe, inda aka halaka mutane da dama tare da sace sama da mata da yara 100.
Sanatan ya bukaci gwamnatin tarayya ta kaddamar da hare-haren tsabtace yankuna da ake zargin ‘yan ta’adda na boyewa, musamman a dajin Sambisa da sauran dazukan da ke fama da matsalar tsaro.
