Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya soki shugabannin Nijeriya saboda, sun fi mayar da hankali kan zaɓen da ke tafe maimakon magance matsalar tsaro da ke ƙara tsananta a ƙasar.
A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na sada zumunta, Obi ya ce ƙasar na cikin mawuyacin hali na tsaro, inda hare-haren ‘yan ta’adda da sace sacen mutane ke ƙaruwa a sassa daban-daban.
Ya kawo misali da hare-haren baya bayannan da aka kai jihar Borno da ya yi sanadiyyar mutane da dama tare da sace mata kusan 100.
Obi ya kuma nuna damuwa kan rahotannin matsalar tsaro a jihohin Nasarawa, Kogi da Benue inda mazauna yankuna ke cewa ‘yan ta’adda suna mamaye gonaki da dazuka, lamarin da ke tilasta wa mutane barin gidajensu.
