Gwamnatin Nijeriya ta fara neman ra’ayoyin jama’a kan yiwuwar yin doka da za su kare yara a intanet, ciki har da kayyade shekarun da yara za su iya amfani da kafafen sada zumunta.
Ministan sadarwa da kirkire-kirkire, Bosun Tijani, ne ya sanar da wannan shiri a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata.
Ya bayyana cewa duk da cewa intanet na ba yara damar koyo, kirkira da sadarwa, amma yana iya jefa su cikin hadurruka kamar cin zarafi a yanar gizo, kallon abubuwan da ba su dace ba, da kuma barazanar da sabbin fasahohi ke haifarwa.
