Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage sauraron shari’ar tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami, tare da dansa Abdulaziz Malami, kan zargin daukar nauyin ta’addanci da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Kotun wadda Justice Joyce Abdulmalik ke jagoranta ta dage shari’ar zuwa ranakun 15 da 16 ga Afrilu, 2026, domin fara sauraron karar.
A zaman kotun da aka yi ranar Talata, lauyan masu gabatar da kara, Akinlolu Kehinde, ya sanar da kotu cewa an ba shi aikin jagorantar shari’ar ne kwanan nan, don haka yana bukatar karin lokaci domin ganawa da shaidu da kuma shirya takardun shari’ar.
Ya ce an ba shi umarnin karɓar shari’ar ne a ranar Litinin, don haka ya bukaci kotu ta ba su sabon lokaci domin su shirya yadda ya kamata.
