Kungiyar lauyoyin gwamnati ta Law Officers Association of Nigeria (LOAN) reshen Kano ta sanar da cewa mambobinta za su shiga yajin aikin sai baba ta gani daga tsakar dare na ranar 11 ga Maris, 2026, sakamakon abin da ta kira rashin magance matsalolin da suke fuskanta a aiki.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta bakin shugabanta,Barista Abdullahi Aminu Shamsu ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan tattaunawa da suka yi da gwamnati lokuta da dama amma ba a warware matsalolin ba.
Kungiyar ta ce tun daga shekarar 2025 take gabatar da koke-koke ga gwamnati, har ma aka kafa kwamiti domin duba matsalolin, sai dai a cewarsa duk da amincewar gwamnati kan wasu shawarwari, har yanzu ba a aiwatar da su ba.
Ya kuma bayyana cewar suna ta fama da shari’u musamman na manyan laifuka da kuma barazana da suke fuskanta daga mutane amma duk da haka hakkinsu na lauya baya fita, wannan dalilin ya sanya kungiyar daukar wannan mataki.
