Shugabancin majalisar dattawan Nijeriya ya cire sunan sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, daga cikin tawagar Nijeriya da za su halarci taron mata na majalisar dinkin duniya da ake gudanarwa a birnin New York, inda aka maye gurbinta da sanata namiji.
Jaridar Premium times ta rawaito cewa taron da aka fara a ranar 9 ga Maris kuma za a kammala 19 ga Maris, inda ake tattauna hanyoyin inganta damar mata wajen samun adalci da kuma kara daidaiton jinsi a duniya.
Sanatar ta bayyana cewa tun da fari ma’aikatar mata ta gayyace ta cikin tawagar Nijeriya, inda aka bukace ta da ta tura bayanan fasfo É—inta na kasa da kasa.
Ta ce ta tura bayanan cikin sa’o’i kadan bayan an bukace ta, amma daga bisani an sanar da ita cewa ba za ta halarci taron ba saboda an ce ta makara wajen tura bayanan.
