Akalla mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da wasu huɗu suka fada hannun masu garkuwa da mutane a hare-hare daban-daban da ‘yan bindiga suka kai a jihohin Kaduna, Kogi da Ondo.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a jihar Kaduna, ‘yan bindiga sun kai hari a unguwannin Titin Bariki da Tsangaya da ke ƙaramar hukumar Makarfi a daren Lahadi tsakanin karfe 9:15 zuwa 10:00 na dare, inda suka halaka wani mutumi tare da sace wata tsohuwa.
A wani hari na daban a jihar Kogi kuma, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani manomi mai suna Raphael yayin da yake aiki a gonarsa kusa da kogin Lawri River a garin Odo‑Ere da ke ƙaramar hukumar Yagba West a ranar Asabar da rana.
A jihar Ondo kuwa, wasu ‘yan bindiga uku dauke da makamai sun sace mutane biyu a wani mazaunin manoma da ke Kajola, a yankin Ilu‑Abo da ke ƙaramar hukumar Akure North.
Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa jami’anta sun fara bincike domin ceto mutanen da aka sace tare da kamo wadanda suka aikata laifin.
