Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da bayar da lasisin shigo da man fetur daga kasashen waje na tsawon wata na biyu, matakin da ke nuna yunƙurin gwamnati na karfafa samar da fetur a cikin gida.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa wannan mataki na zuwa ne yayin da hukumomi suka fara aiwatar da wasu tanade-tanade na dokar masana’antar man fetur, wadda ta tanadi cewa za a ba da izinin shigo da fetur ne kawai idan na cikin gida bai wadatar da bukatar ‘yan kasa ba.
Bayanan da hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta Nijeriya (NMDPRA), ta fitar sun nuna cewa ba a bayar da wani sabon lasisin shigo da fetur ba a watan Fabrairu.
