Saturday, March 21, 2026
HomeLabaraiMinistan tsaron Nijeriya ya kira taron gaggawa da harfsoshin tsaro

Ministan tsaron Nijeriya ya kira taron gaggawa da harfsoshin tsaro

Ministan tsaron Nijeriya, Christopher Musa, ya kira taron gaggawa da dukkan hafsoshin rundunonin soji ofishinsa domin tattauna yadda za a shawo kan hare-haren da ake kai wa sansanonin sojoji a yankin Arewa maso Gabas.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa manyan jami’an tsaron sun hada da babban hafsan tsaro Olufemi Oluyede, da babban hafsan sojin ʙasa, Waidi Shaibu, sauran sun hada da babban hafsan sojin sama, Sunday Aneke, da na sojin ruwa, Idi Abass.

Google search engine

Rahotanni sun ce taron ya biyo bayan sabbin hare-haren da ā€˜yan ta’adda suka kai kan sansanonin sojoji a jihar Borno, inda akalla kwamandoji uku masu manyan suka rasa rayukansu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata