Saturday, March 21, 2026
HomeLabaraiMasu garkuwa da mutane sun nemi naira miliyan 300 na fansar karamin...

Masu garkuwa da mutane sun nemi naira miliyan 300 na fansar karamin yaro da ‘yan uwansa da suka sace a Kaduna

Masu garkuwa da mutane da suka dauke yara 4 a jihar Kaduna sun tuntubi mahaifin yaran tare da neman naira miliyan 300 a matsayin kudin fansa.

Google search engine
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sun yi barazanar kashe karamin yaron dan shekaru biyu saboda kukan da yake yi.
Mahaifin yaran wanda ke zaune a Keke A, karamar hukumar Chikun, ya ce lokacin da suka kira shi yana ji lokacin da suke dukan yaran, ba yadda zai yi.
Yan bindigar sun sace yaran ne a lokacin da mahaifinsu ya ce asibiti domin duba mahaifiyarsu wadda aka kwantar da ita saboda rashin lafiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata