Saturday, March 21, 2026
HomeLabaraiKo kujerar Sanata ba za ka iya ci a jihar Kaduna ba...

Ko kujerar Sanata ba za ka iya ci a jihar Kaduna ba – Fadar shugaban kasa ta sake yi wa El-Rufa’i martani

Google search engine
Mai bai wa shugaban Nijeriya Bola Tinubu shawara kan yada labarai Daniel Bwala, yayi zazzafan martanin ga Nasir El’rufa’i inda yace ko kujerar Sanata Nasiru Elrufa’i ba zai iya ci a Kaduna ba, domin siyasarsa ta labewa cikin rigar wani jagora ce.
Bwala ya yi martanin ne a wata fira da gidan talabijin na TVC, inda ya ce tasirin siyasar El-Rufai yana da nasaba da hadakarsa da wasu jagorori, nasarar da El’rufa’i ya samu a siyasa har ya zama gwamnan Kaduna, ya laɓe ne da guguwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma saboda Buhari ne aka sake zabensa karo na biyu, a don haka a yanzu ba zai iya cin zaben ko da Sanata ba.
A ‘yan kwanakinnan dai tsohon gwamnan jihar Kaduna na yawan sukar gwmnatin shugaba Tinubu da kuma jam’iyyar APC, duk da kasancewarsa dan jami’yyar.

 

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata