DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamna Zulum ya rage farashin fetur zuwa N600 ga manoman dake yankunan da matsalar tsaro ta shafa

-

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya ce gwamnatin jihar za ta rage farashin fetur ga manoma da ke yankunan da matsalar masu tada kayar baya ta shafa.
Zulum ya bayyana hakan ne a jiya Jumu’a, lokacin da yake kaddamar da kayan noma ga manoma 5000 da matsalar tsaro ta raba da gidajensu.
A cewar gwamnan, litar mai da ake saidawa N1,000 zuwa N1,200 a Maiduguri, za a bayar da tallafi don rage farashin ga manoma su rika samu N600, da manufar saukaka musu tsadar kayayyaki da kuma barnar da su ka fuskanta saboda matsalar tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara