Saturday, March 21, 2026
HomeLabaraiGwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sake nada kwamishinoni

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sake nada kwamishinoni

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin wasu mukamai na wasu muhimman mutane a gwamnatinsa ciki har da Ahmad Muhammad Speaker a matsayin mashawarci kan yada labarai.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce sauran mukaman sun hada da Injiya Ahmad a matsayin mai baiwa gwamna shawara bangaren ayyuka da Malam Sani Abdullahi Tofa bangaren ayyuka na musamman.
Gwamnan ya kuma nada Malam Sani Tofa a matsayin Khadi na kotun shari’a, kazalika da da Honarabul Ibrahim Jibrin Fagge a matsayin shugaban hukumar kula da ma’aikatan kananan hukumomi da sai Hajia Ladidi Ibrahim Garko a matsayin shugabar hukumar kula da ma’aikatan jihar Kano.
Sanarwar ta ce, gwamnan zai rantsar da wadanda aka baiwa mukaman a gobe Litinin 6 ga watan Janairun a fadar gwamnatin jihar Kano.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata