DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa’i ya fice daga jam’iyyar APC ya kuma SDP

-

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ya koma jam’iyyar SDP.

Google search engine

Tsohon gwamnan ya bayyana ficewar sa a shafinsa na Facebook yana mai cewa “daga yau 10 ga Maris na shekarar 2025 na fice daga jam’iyyar APC”.

Nasir El-Rufai ya bayyana cewa a shekara biyun da jam’iyyar APC ta yi babu wani abin a zo a gani da ta aiwatar ga ‘yan kasa.

Tsohon gwamnan ya jaddada cewa zamansa na shekaru takwas a matsayin gwamnan jihar Kaduna ya samar da ci gaba a fannin ilimi da kiwon lafiya da ababen more rayuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Fadar Shugaba Tinubu ta soki Atiku kan kwatanta gwamnatinsa da ta mulkin soja

Fadar Shugaban Nijeriya ta caccaki madugun adawa Atiku Abubakar, bisa kwatanta gwamnatin Tinubu da mulkin soja, tana mai bayyana kalaman nasa a matsayin abinda basu...

Majalisar Dattawa ta dakatar da muhawara kan gyaran dokar zabe tare da shiga zaman sirri

Majalisar Dattawan Nijeriya ta dakatar da muhawarar kan kudirin dokar zaɓe ta 2022, domin bai wa ’yan majalisa damar yin nazari mai zurfi kafin ɗaukar...

Mafi Shahara