DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Farashin shinkafar waje mai nauyin 50KG ya karye a kasuwannin Najeriya

-

Rahoton da kamfanin S&P Global ya fitar ya bayyana cewa farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 ya sauka zuwa N58,000 a wasu yankunan Najeriya, musamman a kauyuka, sakamakon yawaitar shigo da shinkafa daga Jamhuriyar Benin.

Google search engine

Wannan na zuwa ne bayan kasar India ta cire harajin fitar da shinkafa irinta parboiled, wanda ya sa kasuwar shinkafa ta Yammacin Afirka ta fuskanci koma baya.

A cikin shekarar 2024 gaba daya, India ta fitar da tan miliyan 5.35, idan aka kwatanta da tan miliyan 3.9 na 2023. Inda rahoton yace har yanzu Najeriya na ci gaba da shigo da shinkafa ta Jamhuriyar Benin ta barauniyar hanya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsare-tsaren Tinubu na farfaɗo da martabar Nijeriya a duniya -Kashim Shatima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce gyare-gyaren da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa na sake gina martabar Nijeriya a idon duniya tare...

Gwamnatin Nijeriya na shirin dakatar da shigo da kayan tsaro daga waje

Gwamnatin Nijeriya ta yi niyyar kera dukkan makami da ake buƙata a cikin gida nan da shekara biyu zuwa biyar masu zuwa. Minista a ma'aikatar Tsaron...

Mafi Shahara