DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamna Nasir Idris na Kebbi ya nesanta kansa daga jita-jitar ficewa daga jam’iyyar APC

-

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya nesanta kansa daga rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa shi da wasu gwamnoni hudu na shirin ficewa daga jam’iyyar APC don shiga wata hadaka da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da wasu ‘yan siyasa ke kokarin kafawa.

Google search engine

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ahmed Idris, ya fitar, Gwamna Idris ya bayyana rahotannin a matsayin karya, da kuma kage, inda ya tabbatar da cewa shi ba dan siyasa ne mai yawo daga jam’iyya zuwa jam’iyya ba.

Gwamnan ya ce “Ina da tushe a APC, ‘jam’iyyar APC ce ta daga ni, kuma ina wa APC hidima,” yana mai jaddada cewa ko da kowa zai fice a jam’iyyar APC, shi ne zai zama na karshe da zai bar jam’iyyar da ta gina shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Hayaniya ta barke a sakatariyar PDP a Abuja

An yi hatsaniya a sakatariyar jam’iyyar PDP da ke Abuja sakamakon yunkurin bangarori biyu na jam’iyyar su gudanar da zaman nasu a rana ɗaya, abin...

Dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore ya yi Allah-wadai da sace dalibai a jihar Kebbi

Dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya yi Allah-wadai da sace ‘yan mata 25 daga Makarantar sakandare ta gwamnati, da ke a Maga, a karamar...

Mafi Shahara