DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnan jihar Ribas Similanayi Fubara ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2025 naira tiriliyan 1.188 awanni 48 bayan gabatarwa majalisar dokokin jihar

-

 

Gwamnan jihar Ribas Similanayi Fubara

Google search engine

A wannan Alhamis, 2 ga watan Janairu, 2025, Gwamnan Ribas Similanayi Fubara ya sanya hannu kan kasafin kudin 2025 tare da godewa majalisar dokokin jihar karkashin jagorancin Victor Oko-Jumbo bisa yin kyakkyawan aikin cikin awanni 48.

Gwamnan ya tabbatar da cewa majalisar dokokin wadda Oko-Jumbo ke jagoranta ita ce daya tilo da ake da ita a jihar.

Sai dai gwamna Fubara ya bayyana cewa Martins Amaewhule da wasu mambobi 26 da suka sauya sheka daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa jam’iyyar APC ba ‘yan majalisa ne ba, duk kuwa da kokarin da suka yi na janye matakin da suka dauka a kwanakin nan.

Gwamna Fubara dai ya shiga takun saka da wasu ‘yan majalisun jihar da ke goyon bayan ministan Abuja Nyesom Wike, wanda daga baya suka bayyana komawar su jam’iyyar APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ma’aikatar tsaron Nijeriya na bukatar ƙwararren shugaba – Shehu Sani

Tsohon dan majalisar dattawan Nijeriya da ya wakilci Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya nuna bukatar samun ƙwararren shugaba da zai jagoranci ma'aikatar tsaron...

Wike na rikewa Tinubu duk filin da gwamnati ta kwace a Abuja – Hadiminsa

Hadimi ga ministan Abuja Nyesom Wike, Lere Olayinka ya bayyana cewa duk wani fili da gwamnati ta kwace iko da mallakarsa a birnin na kasancewa...

Mafi Shahara